Yadda Za'a Kara Kiba Ga Mai Bukatar Hakan Yai Wannan Hadin - Gidan Labarae

Yadda Za'a Kara Kiba Ga Mai Bukatar Hakan Yai Wannan Hadin - Gidan Labarae


1) Domin Karin Kiba, Za'a samo Zabib, da hulba, Za'a wanke Zabib din sannan a zuba shi a cikin ruwa Kofi biyu, sa yayi awa (16) Sannan Amurtsike shi a tace, bayan ya hade sai kuma a zuba hulba cokali (2) idan ruwan yayi kasa Sai a kara wani daga nan sai a sanya a freeze a rufe, amma banda marfin Wanda zai rufe kwanon ko robar gamgam. Idan yakara kamar awa (6)Sai a tace za'a rika shan karamin kofin shayin larabawa ,ko buzaye.



Sai dai yakan sanya kara cin abinci, to ana bukatar a rika cin abinci mai kyau Wanda yake gina jiki.



(2) hanya ta biyu:



(1) Yayan hulba

(2) alkama

(3) waken suya

(4) gyada

(5) garin dabino

(6) garin farar shinkafa

(7) madara

(8) zuma



Sai ki maida su gari suyi laushi sai ki rika diba cokali daya ana soya kwai dashi man suyar yakasance danyan man zaitun ne. Yadda za'a sarrafa su, zaki samu alkama da farar shinkafa ki jikasu sai sun kwana sai ki shanyasu subushe sannan ki kai a nika sannan ki samu garin Dabino sannan gyada ma a soya ta



Sama samansa sannan ki nika sai ki hada garukkan waje guda sannan ki debi cokali 2 ki zuba ruwan rabin kofi sannan ki dora akan wuta har ya tafasa. 



Sai ki sauke kisa madara ta ruwa ko ta gari da zuma sai ki hada ki rinka sha musamman idan zaki kwanta barci cikin kankanin lokaci za kiyi kiba sumul fatarki ta canza.


Post a Comment

Previous Post Next Post